Uwa jam’iyyar APC ta kasa a wani yunkuri na sasanta bangarorin biyu da ke rikici da juna a jihar Kano, ta sake yin wani taron tattaunawa ranar Talata.

Solacebase ta ruwaito cewa taron sulhun ya gudana ne a Abuja karkashin jagorancin shugaban riko na jam’iyyar tare da Sanata Ibrahim Shekarau, Barau I. Jibrin, Kabiru Gaya da ‘yan majalisar wakilai da suka hada da Yakubu Dogara, Alhassan Ado Doguwa Shaaban. Ibrahim Sharada, Abdulkadri Jobe da Ali Wudil da dai sauransu.












































