Wani sabon rahoto ya nuna cewa hukuncin kisa a ƙasar Saudiyya ya ninka a ƙarƙashin jagorancin Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman.
Wata ƙungiya mai rajin kare hakkin bil-dama ta ce 11 daga cikin waɗanda aka kashe tun bayan da aka naɗa shi a kan gadon Yarima mai jiran gado a shekarar 2015 yara ne, lokacin da aka fara tsare su.
Rahoton ya ce an kashe mutum 81 a cikin kwana ɗaya a watan Maris ɗin bara.
‘Yan uwan wasu daga cikin waɗanda aka kashe sun shaida wa BBC cewa ba a sanar da su cewa za a kashe ‘yan uwan nasu ba.













































