Wasu na jikin Buhari na yi wa takarar Tinubu zagon-ƙasa – El-Rufai

Nasir El Rufai 1
Nasir El Rufai 1

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa wasu dakaru a fadar shugaban kasa na kokarin taɗile nasarar ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a zabe mai zuwa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Laraba lokacin da ya bayyana a shirin Barka da Hantsi na gidan talabijin na Channels TV.

Yayin da ya amince cewa cewa akwai rashin jituwa a cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Mista El-Rufai ya bayyana cewa wasu dakarun da ‘yan takararsu suka sha kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, sun ki amincewa da shan kaye, don haka suka kuduri aniyar yin yaki da jam’iyyar da kuma sanya ta fadi zabe. .

El-Rufai ya ce, “Na yi imanin cewa akwai wasu mutane a Villa (Aso Rock) da ke son mu fadi zabe, sun samu dan takararsu, kuma dan takarar bai ci zaben fidda gwani ba…”

“Suna kokarin ganin mun fadi zabe ne, kuma suna fakewa da burin shugaban kasa na yin abin da yake ganin ya dace.

“Zan ba da misali guda biyu: wannan tallafin man fetur da ake kashewa kasar tiriliyoyin Naira, wani abu ne da muka amince a cire,”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here