A ranar Litinin ne kotun masana’antu ta kasa da ke Abuja, ta sanya ranar 6 ga watan Afrilu domin sauraren karar da aka shigar kan shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, Chris Isiguzo.
Mai shari’a Osatohanmwen Obaseki-Osaghae ya dage ci gaba da sauraron karar bayan lauyan mai kara, Obinna Okeke ya bukaci sanya wata ranar don fara sauraren karar.
Tunda lauyan wadanda ake kara, Patrick Ediale, bai yi adawa da bukatar ba, sai mai shari’a Obaseki-Osaghae ya sanya ranar 6 ga watan Afrilu domin sauraron karar.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (
NAN ya ruwaito cewa Mista Akindele Orimolade, Editan Jaridar New National Star Newspaper, ya maka kungiyar NUJ da Isiguzo a gaban kotu a matsayin wadanda ake tuhuma na 1 da na 2.
A cikin takardar sammaci mai lamba: NIC/ABJ/257/2021 mai kwanan ranar 20 ga Satumba, 2021 da Okeke, lauya ga Orimolade, ya shigar da ranar 27 ga Satumba, 2021, lauyan ya yi addu’a ga kotu da ta bayyana cewa “bisa ga “Sharidu na 3 () 1) (a) (2) (b) na Kundin Tsarin Mulki na NUJ na Nuwamba 15, 2011, Isiguzo ba cikakken memba ne a NUJ.
Lauyan ya roki ga kotun da ta dawwamar da doka, tare da hana Isiguzo bayyana kansa a matsayin shugaban NUJ na kasa kuma ya daina shiga duk wata harka ta kungiyar “gaba daya, ta kowace hanya.
A cikin bayaninsa na gaskiya da ke tabbatar da dalilin daukar matakin, Orimolade ya bayyana Isiguzo a matsayin “dan jarida mai yaudara.”
A cewarsa, shi (Isiguzo) bai mallaki mafi karancin cancantar ilimi ba kuma bai cika wasu sharudda da kundin tsarin mulkin wanda ake kara na daya ya bukata ba na sanya shi mamba na 1 da ake kara domin ya bashi damar tsayawa takara kuma a zabe shi a matsayin Shugaban kasa na yanzu a zaben NUJ na kasa daga 4 zuwa 5 ga Oktoba, 2018.
Ya kara da cewa kafin zaben NUJ, Isiguzo ya shiga cikin badakalar satifiket din bogi wanda har zuwa lokacin shigar da karar ba a wanke ba.













































