Majalisar wakilai ta ƙasa ta amince da gudanar da bincike kan hukumar shirya jarabawa ta (NECO) bisa zargin kashe kuɗaɗen gwamnati ba tare da samun izinin da doka ta tanada ba.
Wannan mataki ya biyo bayan kudirin da ɗan majalisa Amobi Ogah daga jam’iyyar Labour Party (LP) mai wakiltar Abia ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis.
Ogah ya bayyana cewa binciken ya yi daidai da tanade-tanaden sashe na 88 da 89 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, wanda ya baiwa majalisar ikon kira ko neman takardu daga kowace ma’aikata ko hukuma ta gwamnati domin tabbatar da gaskiya.
Ya ce NECO, a matsayinta na hukuma mai zaman kanta da ke samar da kuɗaɗen shiga ga ƙasar nan, dole ne ta kasance mai bayyana yadda take amfani da waɗannan kuɗaɗe a bainar jama’a.
Karin labari: Emefiele: Kotu ta amince a gabatar da tattaunawar WhatsApp cikin zargin almundahanar dala biliyan 4.5
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa ɗan majalisar ya nuna damuwa kan yadda NECO ke aiwatar da sauya tsarin kashe kuɗi (virement) ba tare da samun amincewar majalisar ba, yana mai cewa hakan saba wa kundin tsarin mulki ne.
A cewarsa, dole ne a binciki yadda hukumar ta aiwatar da kasafin kuɗinta da kuma kuɗaɗen da ta samu daga cikin gida daga shekarar 2023 zuwa yau, tare da duba bayanan asusun bankinta da kuma hujjar yadda take tura kuɗaɗe zuwa asusun baitulmalin ƙasa.
Mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman, ya umurci kwamitin majalisar kan ilimi da hukumomin jarabawa da ya gudanar da cikakken bincike kan lamarin, sannan ya gabatar da rahoto cikin makonni uku.












































