Osinbajo ya soki bangaren shari’a, tare da zargin kotun koli da rashin samar da daidaito

Yemi Osinbajo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya soki kotun koli bisa abin da ya bayyana da rashin daidaito da kuma dogaro da ƙa’idojin fasaha fiye da bin ainihin adalci.

Osinbajo, wanda lauya ne, ya bayyana hakan a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, a yayin laccar shekara-shekara karo na biyu da aka shirya a ƙarƙashin sunan Farfesa Yusuf Ali a Jami’ar Jihar Kwara da ke Malete.

Ya ce tsarin shari’a na Najeriya na buƙatar sauyi mai zurfi domin daidaita shi da bukatun al’umma, ba wai ci gaba da fifita tsauraran ƙa’idoji ba.

Osinbajo ya bayyana cewa tsarin adalci ya kamata ya zama don hidimar jama’a, ba don nuna ƙwarewa a kan ƙa’idoji marasa amfani ba, yana mai cewa kotunan Najeriya, musamman kotun koli, sun fi karkata zuwa tsari fiye da ma’ana.

Ya ƙara da cewa wannan matsalar tana jawo raguwar amincewar jama’a ga tsarin shari’a tare da hana gaskiya ta tabbata, duk da cewa kotun koli a wasu lokuta ta nuna sassauci, musamman a shari’o’in zaɓe.

A nasa ɓangaren, Farfesa Chidi Odinkalu, wanda ya gabatar da jawabin babban bako mai taken “Hanyar kawar da al’adun mulkin mallaka a shari’a: aiwatar da dokar ƙasa don amfanin lauyoyin Najeriya”, ya bayyana cewa tsarin shari’a na ƙasar har yanzu yana daure da tsofaffin al’adun Turawa da ya kamata a kawar da su.

Shi ma shugaban jami’ar KWASU, Farfesa Jimoh Shaykh-Luqman, ya bayyana cewa an kammala shirye-shiryen gina sabbin gine-ginen makarantar horar da lauyoyi ciki har da babban ɗakin taro da ɗakunan karatu masu ɗaukar ɗalibai da dama.

Mai masaukin baki kuma lauya Farfesa Yusuf Ali (SAN) ya jaddada bukatar Najeriya ta samar da wani abu da zai haɗa ƙasa ɗaya, yana mai cewa rashin haɗin kai da bambance-bambancen siyasa da kabilanci suna ci gaba da hana cigaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here