Hukumar Kwastam ta Ƙasa ta sanar da ranar 14 ga Oktoba a matsayin ranar gudanar da jarrabawar daukar ma’aikata ta kwamfuta (CBT) ga masu neman aiki a matakin Superintendent Cadre a faɗin yankuna shida na ƙasar.
Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na X da kuma Facebook a ranar Juma’a, inda ta ce jarrabawar za ta gudana a lokaci guda a jihohin da aka ware, bisa ga jihohin asalin kowanne ɗan mutum guda.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa waɗanda za su rubuta wannan jarrabawa su ne waɗanda aka tabbatar da takardunsu kuma suka kammala jarrabawar gwaji ta farko da ta kai tsaye.
NAN ta ce, an gudanar da jarrabawar daukar ma’aikata ta matakan Inspectorate da Customs Assistant a ranar 9 ga Oktoba.
Hukumar ta bayyana cewa waɗanda suka ci gaba daga matakai na baya za su shiga shafin updates.customs.gov.ng ta amfani da lambar NIN domin duba cikakkun bayanan jarrabawarsu da wuraren da aka ware musu.
Hukumar ta gargadi masu neman aikin da su buga takardun shaidar jarrabawarsu a launin da aka tsara domin gabatarwa a wuraren jarrabawar, tare da tabbatar da cewa kowanne ɗan takara ya je wurin da aka ware masa kawai, domin rashin bin umarnin zai iya jawo masa ƙin karɓa.
Za a gudanar da jarrabawar a cibiyoyin da aka ware kamar haka: Lagos da Osun (Kudu maso Yamma), Enugu da Abia (Kudu maso Gabas), Rivers da Edo (Kudu maso Kudu), Abuja da Kwara (Arewa ta Tsakiya), Bauchi da Adamawa (Arewa maso Gabas), sannan Kaduna da Sokoto (Arewa maso Yamma).
Hukumar ta jaddada cewa wannan mataki na jarrabawar na musamman ne ga waɗanda suka ci gaba daga matakin Superintendent Cadre kawai.













































