Emefiele: Kotu ta amince a gabatar da tattaunawar WhatsApp cikin zargin almundahanar dala biliyan 4.5

Emefiele court new 750x430

Wata kotu ta musamman dake Ikeja a jihar Legas ta amince da gabatar da tattaunawar WhatsApp a matsayin hujja a shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, bisa zargin almundahana da cin hanci da rashawa da ta kai dala biliyan 4.5 da kuma naira biliyan 2.8.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa mai shari’a Rahman Oshodi ne ya yi watsi da ƙin amincewar lauyoyin Emefiele, inda ya amince da gabatar da tattaunawar WhatsApp da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta miƙa a matsayin hujja, wadda aka sanya mata suna “Shaida G”.

Haka kuma kotun ta karɓi wasu wayoyi da aka miƙa a matsayin hujjoji cikin shari’ar. Emefiele yana fuskantar tuhuma guda 19 da suka shafi karɓar rashawa da cin zarafin mukami, yayin da abokin shari’arsa Henry Omoile ke fuskantar tuhuma uku kan karɓar kyauta ta haram.

Lauyan EFCC Rotimi Oyedepo (SAN) ya ci gaba da gabatar da shaidarsa, mai suna Alvan Grumnaan, wanda ya bayyana cewa bincikensu ya gano tattaunawar WhatsApp tsakanin Omoile da wani John Adetola, inda suka tattauna batun bayar da dala 400,000 ga “oga” wato Emefiele.

Grumnaan ya bayyana cewa Adetola ya tabbatar da kai kuɗin ga wani mai suna Ikechukwu-Ayoh, wanda shi ne mataimakin Emefiele a lokacin, domin ya mika masa kuɗin a ofishin CBN dake Legas.

Haka kuma ya ce akwai wata mu’amala ta dala 200,000 da aka mika ta hanyar Ikechukwu-Ayoh zuwa hannun Emefiele.

Karanta: Bayan yafiyar shugaban ƙasa, tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan ya ce “Allah ne ya yi amfani da Tinubu wajen nuna mini rahama”

Shaidar ta ƙara bayyana cewa wani mai kwangila a CBN mai suna Victor Oyedua ya tabbatar da cewa shi ne ya bayar da waɗannan kuɗaɗe domin a taimaka masa samun biyan kuɗin ayyukan da ya kammala a bankin, inda duk bayanansa aka rubuta.

Kotun ta kuma karɓi wasu takardu daga Babban Bankin Najeriya a matsayin hujja “H”, duk da ƙin amincewar lauyoyin Emefiele Olalekan Ojo (SAN) da Kazeem Gbadamosi (SAN), waɗanda suka ce takardun ba su da sahihanci.

Haka kuma an karɓi wayar John Adetola nau’in MI10T a matsayin “Shaida I”, wadda ke ɗauke da tattaunawar WhatsApp da aka gabatar a gaban kotu.

Lauyan EFCC ya ƙara miƙa wasu bayanai da aka samu daga mai laifi na biyu yayin bincike, duk da cewa lauyoyin kariya sun ce an tilasta masa ya bayar da bayanan.

Mai shari’a Oshodi ya dage ci gaban shari’ar zuwa ranar 21 ga Nuwamba domin sauraron rahoton binciken na’urorin da ɓangarorin suka amince a gwada, sannan ya sanya ranar 2 ga Disamba domin ci gaba da shari’ar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here