Gwamnatin jihar Kano ta kara zage damtse wajen karfafa manufofin muhalli da sauyin yanayi, tare da jan hankalin masu ruwa da tsaki don samar da ci gaba mai dorewa.
A wata sanarwa da kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano, Dakta Dahir M. Hashim ya fitar a ranar Asabar din da ta gabata, ya bayyana cewa tawagarsa ta halarci wani horo da kungiyar Black Forest da kungiyar raya masana’antu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIDO) suka shirya.
SolaceBase ta ruwaito cewa horon ya mayar da hankali ne kan samar da tsarin sarrafa sharar gida na kayan amfani da makamashin da ake amfani da su a waje, wani muhimmin mataki na samun ci gaban tattalin arziki a Kano da ma Najeriya baki daya.
Sanarwar ta ce a ziyarar da kwamishinan da tawagarsa suka kai, sun tattauna da daraktan kula da kare muhalli da ma’aikatar muhalli ta tarayya, Engr. (Dr.) Bahijjatu Abubakar kan batutuwan da suka shafi muhalli.
A cewar sanarwar, tattaunawar tasu ta ta’allaka ne kan yadda ake sarrafa shara, da tsare-tsare na sharar fage, da magance gurbatar yanayi.
Tawagar ta gana da, Darakta Janar na Majalisar kula da sauyin yanayi na kasa, Nkiruka Maduekwe, domin daidaita manufofin sauyin yanayi na Kano da kungiyar NDC ta kasa baki daya da kuma samar da wani tsari mai inganci.
Sauran batutuwan daka gabatar sun hada da tattaunawa da kungiyar eHealth Africa don binciken haɗin gwiwa tare magance matsalolin da suka shafi lafiya da sauyin yanayi, da nufin samar da cikakkeb tsari ga dorewar muhalli.
Dakta Hashim ya jaddada kudirin gwamnati na mai da Kano ta zama cibiyar kula da ayyukan yanayi da dorewar muhalli a matakin kasa da kasa.