NAHCON ta gyara kwangilar aikin Hajjin 2025 da kamfanin Mashariq Al-Dhabia cikin sauki

NAHCON Chairman Prof Abdullahi Saleh Usman sabo 750x430 (1)

Hukumar kula da Alhazai ta ƙasa NAHCON ta yi gyara ga kwantiragin da ta kulla da Mashariq al Dhabia, kamfanin da zai yi hidima a kasar Saudiyya ga maniyyata domin tabbatar da aikin Hajjin bana na 2025 ba tare da cikas ba.

Shugaban hukumar ta NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman ne ya sanya hannu kan gyaran kwangilar a madadin hukumar, yayin da Muhammad Hassan shugaban kamfanin Mashariq al Dhabia ya sanya hannu a madadin kamfanin.

Usman ya bayyana cewa an yi gyaran ne domin inganta shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025, tare da tabbatar da tafiyar da alhazan Najeriya cikin nasara.

Karin karatu: Dalilin da ya sa NAHCON ta zaɓi wani kamfani don yi mata aikin hajjin 2025 – Mahukunta

Ya karyata jita-jitar da ake ta yadawa game da soke kwangilar, inda ya bayyana cewa gyaran da aka yi na da nufin inganta ayyukan alhazai a lokacin aikin Hajji.

Ya kara da cewa tawagar kamfanin karkashin jagorancin Hassan sun kai ziyarar ban girma a hedikwatar NAHCON domin kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji mai zuwa.

Hassan, ya nuna godiya ga Allah da ya yi tafiya lafiya daga Makka zuwa Najeriya, ya yi alkawarin samar da ingantattun ayyuka ga alhazan Najeriya a lokacin aikin Hajji.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here