Balogun Ajikobi na masarautar Ilorin, Alhaji Isiaka Okunrinjeje, ya rasu.
Okunrinjeje ya rasu ne da sanyin safiyar Lahadi a asibiti, sakamakon rashin lafiya, kamar yadda wata majiya mai tushe ta tabbatar.
SolaceBase ta ruwaito cewa Balogun Ajikobi yana daya daga cikin sarakunan masarautar Ilorin.