Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kori shugabannin jam’iyyar ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark, tare da soke dukkan matakan da suka dauka a jam’iyyar.
Matakan da aka soke sun hada da tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a babban zaben 2027.
Read also: Mutane sun yi biris da dokar hana fita daga gida a Kano
Atiku, wanda a baya Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta wallafa sunansa a matsayin dan takarar shugaban kasa, wanda ya riga ya zabi tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa.
Sai dai, a hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke a ranar Alhamis, kotun ta ayyana kwamitin rikon kwarya na ADC karkashin jagorancin Sanata Mark a matsayin wanda ya saba wa doka.
Kwamitin ne ya shirya zaben fidda gwani wanda ya samar da Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Kotun ta ce ta gamsu da karar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar.
Gombe ya garzaya kotu ne domin kalubalantar tsarin da kwamitin karkashin jagorancin Sanata Mark ya bi wajen karbar shugabancin jam’iyyar.
Ya bayyana cewa, bayan murabus din tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Chief Ralph Nwosu, shi ne ya cancanci karbar shugabancin jam’iyyar.
Read also: Gwamna Yusuf ya bayyana alhini kan rasuwar malamin sadarwa na BUK
Saboda haka, ya bukaci kotun da ta soke dukkan matakan da shugabancin Sanata Mark ya dauka a jam’iyyar, da sauran bukatu.
Wadanda aka lissafa a matsayin wadanda ake kara a shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025 sun hada da ADC, INEC, Sanata Mark, Ogbeni Rauf Aregbesola da Chief Ralph Nwosu.
Mai karar ya kuma bukaci kotun da ta hana Sanata Mark da Aregbesola ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa da sakataren jam’iyyar.
Kotun ta amince da hujjojin mai karar, tare da bayar da dukkan bukatun da ya gabatar.
Hukuncin na iya haifar da jerin sauye-sauye da ɗaukar matakan siyasar kasar, musamman ganin cewa an tsara gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 16 ga Janairu, 2027.
Tuni dai ADC ta sha alwashin daukaka kara kan hukuncin.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, Sakataren Jin Dadin Jama’a na Kasa na ADC, Mista Nkemakolam Ukandu, wanda daga baya aka shigar a shari’ar a matsayin mai ruwa da tsaki, ya ce za su kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara.
Read also: Trade | FB88 – Thế Giới Giải Trí Đỉnh Cao – Khám Phá Ngay Tại Https//fb88.photo | 46-2025
Wannan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan dan takarar jam’iyyar, Atiku, ya gudanar da gagarumin gangamin yakin neman zabe a Jihar Sokoto, a wani bangare na yakin neman zabensa na shugaban kasa na 2027.












































