Mutane sun yi biris da dokar hana fita daga gida a Kano

20240803 110048 1 768x576

Bayan saka dokar hana fita ta sa’o’i 24 da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sanya a Kano tun ranar Alhamis bayan zanga-zangar da aka yi a fadin kasar nan, mutanen kano basu mai da hankali ba kan dokar, inda wasu sukai biris da ita.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa zanga-zangar da aka yi ranar Alhamis a Kano wadda ta janyo wawushe dukiyar jama’a da na Gwamnati da suka kai biliyoyin Naira, lamarin da ya sa gwamnan jihar ya ayyana dokar ta-baci ta sa’o’i 24.

20240803 110125 2 768x576

Rundunar ‘yan sandan jihar a ranar Juma’a ta gurfanar da wasu mutane 320 da ake zargi da yin fashi da makami da barna da wasu kayayyakin da aka sace.

Sai dai gwamnati ta sassauta dokar na tsawon sa’o’i biyar a ranar Juma’a daga karfe 12:00 na rana zuwa karfe 5:00 na yamma domin mazauna jihar su samu damar halartar Sallar Juma’a da rana.

20240803 105035 6 768x576

An ga shingayen binciken ‘yan sanda tare da kungiyoyin sa kai a kan manyan tituna a cikin babban birni suna kokarin tabbatar da bin dokar.

Sai dai kuma a kan titin Ibrahim Taiwo da titin Bello, an bude wasu shaguna domin gudanar da harkokin kasuwanci.

20240803 110048 1 768x576 20240803 110625 768x721

SolaceBase ta ga galibin manyan titunan garin da ‘yan ababan hawa sannan wasu mazauna garin na tattaki zuwa wurare daban-daban.

Hakazalika, an kafa wata kasuwa ta wucin gadi a Sabon Gari ta hanyar New Road tana ci, inda yan kasuwar ke cigaba da saye da sayarwa a gurin.

Daya daga cikin masu cin kasuwar da ta zanta da jaridar SolaceBase, Ifeoma Okechukwu ta ce ta zo ne ta sayo barkono da gari domin suyi amfani dashi a gida.

“Bin dokar hana fita a gida yayi mana wuya tun da aka fara a ranar Alhamis, domin samun kudin sayen abincin da za mu ci abun ba’a cewa komai.” in ji Ifeoma.

20240803 111600 768x576 20240803 105036 1 750x430

“Ina aiki a wani gidan cin abinci, kuma an rufe shagon tun ranar Alhamis da yamma lokacin da aka sanar da dokar hana fita, don haka babu abin da za mu ci gaba da rayuwa tun lokacin.”

’Yan sanda sun kama wasu matasa a hanyar filin jirgin sama, wadanda suka yi ikirarin cewa za su halarci bikin daurin aure a kewayen Brigade a karamar hukumar Nasarawa.

Daga baya an bar su su ci gaba da tafiya

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here