
Hukumar FRSC ta ce akalla fasinjoji 10 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da tirelar DAF akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Jami’in kula da ilimin jama’a na Corps, Jonas Agwu, ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja, inda ya ce hatsarin na ranar Litinin ya biyo bayan gudun wuce gona da iri.
A cewarsa, direban motar ya rasa yadda ya kamata, inda ya fada cikin wani rami da misalin karfe 10:30 na safe tare da dukkan fasinjoji 172 da ke cikin motar.
Karin labari: Jiragen yaƙin Turkiyya sun kashe farar hula 18 a kudancin Somaliya – Al-Shabab
Agwu ya ce 10 daga cikin fasinjojin sun mutu yayin da 48 suka samu raunuka.
Ya ce, tawagar ceto FRSC ta kwashe mutanen zuwa asibitocin St. Anthony da Umaru Musa Yar’adua da ke Kaduna.
Ya kara da cewa, “Hukumar FRSC na ci gaba da kokarin bin diddigin wadanda suka jikkata a asibitoci domin ganin sun samu kulawar da suka dace.
Karin labari: ‘Yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya a Bauchi
Agwu ya rawaito shugaban rundunar Corps, Mista Dauda Ali-Biu yana kira ga dukkan kwamandojin sassan kasar da su karfafa aikin tabbatar da tsaro a fadin kasar nan da kuma yaki da mugun gudu da wuce sa’a da kuma tukin ganganci.
Ali-Biu ya ce dole ne su kuma gargadi direbobin tireloli da su guji kai mutane saman kaya a cikin motocinsu.
Ya umarci kwamandojin da su fara gudanar da ayyukan sintiri na dogaro da kai tare da kotunan tafi-da-gidanka tare da muhimman hanyoyi nan take kamar yadda NAN ta bayyana.












































