‘Yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya a Bauchi

Alhaji Badamasi, 'yan bindiga, kashe, hakimi, basarake, gargajiya, bauchi
'Yan bindiga sun kashe hakimin kauyen Riruwai da ke gundumar Lame a masarautar Bauchi na karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi, Alhaji Garba Badamasi, da suka...

‘Yan bindiga sun kashe hakimin kauyen Riruwai da ke gundumar Lame a masarautar Bauchi na karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi, Alhaji Garba Badamasi, da suka yi garkuwa da shi.

An bayyana cewa wanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, a ranar juma’ar da ta gabata ne suka shiga kauyen, inda suka yi ta’addanci ta hanyar harbe-harbe kafin su kutsa kai cikin fadar hakimin kauyen suka yi awon gaba da shi.

Karin labari: Sojojin Habasha sun kashe mayakan sa kai 150 a Amhara

An ce wadanda suka yi garkuwa da su ba su tuntubi ko daya daga cikin iyalansa ba domin a biya su kudin fansa.

Daga baya ne wadanda suka shiga nemansa suka tsinci gawarsa a cikin dajin da ke kewayen kauyen.

Daga nan ne aka kawo gawarsa fadar Hakimin Lame da ke Gumau a ranar Lahadi 17 ga watan Maris domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Karin labari: An rufe makarantu a Sudan ta Kudu saboda matsanancin zafi

Daya daga cikin masu rike da sarautar kauyen ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai tare da nemawa mamacin rahamar Allah (S.W.T).

Hukumomin ‘yan sandan dai har yanzu ba su magantu game da wannan batu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here