Gwamnatin sojin Nijar ta katse huldar diflomasiyya da Najeriya, Togo, Amurka da kuma ta fuskar tsaro da tsohuwar uwargijiyar kasarsu Faransa.
Kwana biyu ke nan bayan gwamnatin Nijar ta ce babbar makwabciyarta Najeriya ta katse wutar da take ba ta, lamarin da ya sa biranen Yamai, Maradi, Zinder da sauran sassan kasar cikin matasalar wutar lantarki da ba su saba ba a baya.
Gwamnatin sojin Nijar din ta kuma ki ganawa da wakilan da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS), ta tura domin tattaunawa da ita.
Wani daga cikin wakilan ya shaida dawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kasa da awa 24 da isarsu birnin Yamai suka baro kasar Nijar, “ko kwana ba mu yi ba,” ballantana ganawa da Janar Abdourahamane Tiani kamar yadda aka tsara.
A ranar Laraba ne ECOWAS ta tura wakilan nata, karkashin jagorancin tsohon shugaban mulki sojin Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, domin tattaunawa da gwamnatin sojin da ta yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki.
Da farko dai gwamnatin Najeriya ta sanar cewa kwamitin na Abdulsalami Abubakar zai gana da Janar Tiani inda zai gabatar wa gwamnatin sojin da ta yi juyin mulki a Nijar bukatun ECOWAS.
Kungiyar wadda Shugaan Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu yake jagoranta, ta kakaba wa gwamnatin sojin ta Nijar takunkumin karya tattalin arziki, sannan a ranar Lahadi ta ba wa sojojin wa’adin mako guda su mika wa Bazoum mulkinsa.













































