Gwamnatin Kano ta amunce da kashe biliyan 7 domin aiyukan raya kasa a jihar

Abba Kabir Yusuf 723x430 1
Abba Kabir Yusuf 723x430 1

Gwamnatin Jihar kano ta amunce da kashe naira biliyan 7 domin aiyukan raya kasa a fadin jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Halilu Dantiye, ne ya bayyanawa manema labarai hakan ranar Alhamis, bayan taron taron majalisar zartaswa da ake duk mako.

Dantiye ya ce an amunce da kashe kudin ne bayan zama na uku da majalisar zartaswar tayi domin gudanar da wasu mahimman aiyuka a jihar.

Ya kara da cewa an amuncewa hukumar aiyuka da gidaje N1.6 biliyan domin gina sababbin ofisushi da kuma wasu mahimman aiyuka a gidan gwamanati jihar.

Ragowar kudin za’a kashe su ne a kan wasu mahimamna aiyuka a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here