Buhari Ya Nemi Amincewar Nada Mutum 12 A Hukumar kulada Yankin Arewa Maso Gabas.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa da ta tabbatar da nadin mutane 12 a matsayin mambobin hukumar gudanarwar hukumar raya yankin arewa maso gabas ta NEDC.

A cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar a Abuja, bukatar shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan mai kwanan ranar 3 ga watan Mayu.

“A bisa tanadin sashe na 1, sashe na 2(5) (b) na dokar kafa hukumar raya yankin arewa maso gabas ta shekarar 2017, na ke neman majalisar da ta tantance sunayen mutane 12 kamar yadda aka tsara a kasa. a kwamitin gudanarwa hukumar raya arewa maso gabas.

Wadanda aka nada sun hada da: Bashir Bukar Baale, Shugaban (Arewa maso Gabas, Yobe); Suwaiba Idris Baba, Babbar Darakta a harkokin jin kai, (Arewa maso Gabas, Taraba); Musa Yashi, Babban Daraktan Gudanarwa da Kudi, (Arewa Maso Gabas, Bauchi) da Dr Ismaila Maksha, Babban Daraktan Ayyuka (Arewa Maso Gabas, Adamawa).

Sauran su ne: Umar Hashidu, (Arewa maso Gabas, Gombe); Grema Ali, mamba, (Arewa maso Gabas, Borno); Onyeka Bishara-Tony, memba, (Kudu maso Gabas); Mrs Hailmary Ogolo Aipoh, memba, (kudu maso kudu) da Air Commodore Babatunde Akanbi mai ritaya, memba, (kudu maso yammaci).

Sauran wadanda aka zaba sun hada da, Mustapha Ahmed Ibrahim, mamba, (Arewa maso Yamma); Hadiza Maina, mamba, (Arewa ta tsakiya) kuma wakili daga ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa.

Shehu ya ambato cewa shugaban kasar yana mai fatan cewa bukatarsa ​​za ta samu ganin an tantance tare da tabbatar da su kamar yadda majalisar dattawa ta saba.” (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here