Rundunar yan sandan jihar kano tayi nasarar kama wani matashi mai suna Ibrahim Musa dan shekaru 22 a duniya, dake unguwar Rimin kebbe, a karamar hukumar Nasarawa. da ake zarginsa da kashe mahaifiyarshi da wuka.
Jaridar solacebase ta ruwaitu cewa kwamishinan yan sandan jihar kano Mohammed Usaini ya bada umarnin kamo Ibrahim musa wanda ake zargi da kashe mahaifiyarsa mai suna Hajara mohammed.
”A ranar uku ga watan mayu, da misalin karfe 6 na yamma, mun samu rahotan cewa wani matashi mai suna, ya kashe mahaifiyarshi da wuka, sanan ya tsere. Inji Jami’in hurda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da kama matashin ne a yau juma’a yace inda ya ce sun sami nasarar kamashi a karamar hukumar Dawakin tofa da misalin karfe karfe 10 na daren jiya Alhamis













































