Kotu ta sa ranar da zata fara sauraren karar da  dakataccen kwamishinan zaben Adamawa ya shigar da INEC.

Adamawa REC Barr. Hudu Yunusa Ari 600x430 1
Adamawa REC Barr. Hudu Yunusa Ari 600x430 1

Babban kotun tarayya dake zaman ta a Abuja ta tsayar da 1 ga watan yuni, na shekarar 2023, domin fara sauraren karar da dakataccen kwamishinan zaben Adamawa, Hudu Yunusa-Ari  ya shigar da hukumar zabe ta kasa INEC.

A cikin karar da ya shigar ya bayyana dalilan da suka sa ya bayyana Sanata Aisha Dahiru Ahmed (Binani) a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa a zaben da ya gabata.

A cikin karar da lauyanshi Jibrin Okutepa ya mika wa kotun, ya ayyana Binani ne bisa doka da kuma ikon da yake dashi a matsayinshi na kwamishina.

Dakataccen kwamishinan zaben, wanda yake hannun ‘yan sanda a yanzu haka, ya kara da cewa ya yi hakan ne saboda ya kawo karshen karya doka da magudi a gabar sanar da zaben.

Ari ya bukaci dokar kasa ta bawa hukumar zabe ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki umarnin bashi hakuri a bayyanar jama’a kamar yadda tayi wajen bata mishi suna.

Yana neman a wallafa ban hakurin a manyan jaridu guda biyu “dan wanke ni daga cin zarafin da akayi a manyan jaridun kasar nan, dan kawai na yi aikina kamar yadda doka ta bani dama.”

A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/563/2023, Ari ya nemi kotu da ta hana wadan da ake kara da sake kiran taron ‘yan jaridu akan shi.

Ya kuma kara da cewa a cikin karar da ya shigar kafin ‘yan sanda su kama shi, akwai kwamishinoni guda biyu da bai bayyana sunayen su ba, da yake zargin su da yi mishi dan waken zagaye a lokacin zaben cike gurbin da aka yi a Adamawa, bisa wata manufa tasu ta daban.

Wadanda Hudu yake kara sune hukumar shirya  zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, babban supetan ‘yan sanda na kasa, ministan shara’a, da kuma shugaban yan sanda na farin kaya DSS.

Bayan kotu ta kira karar, lauyan shi okutepa ya sanar da kotu cewa dukkanin wadanda ake kara sun karbi sammacin kotun amma kuma hakan bai sa sun halarci zaman ba.

Inda ya kara da cewa suna da damar kwana biyar don mayar da martani, wannan dammar kuma ta kare a ranar 3 ga watan Mayu, inda ya nemi kotu ta dage karar zuwa gajeren lokaci domin sake sauraren karar.

Duba da wannnan ne yasa, mai shari’a James Omotosho ya daga sauraren karar zuwa 1 ga watan Yuni, tare da umarnin sake mika takardar saurare zuwa ga wadanda ake kara.

 

 

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here