“Dalilin da yasa na fice daga APC” – Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyya

APC, Tsohon, Mataimakin, Shugaban, Jam'iyya
Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa Salihu Mohammed Lukman, ya fice daga jam’iyyar. Lukman, wanda tsohon mamba ne na kwamitin ayyuka na...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa Salihu Mohammed Lukman, ya fice daga jam’iyyar.

Lukman, wanda tsohon mamba ne na kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC) a wata sanarwa a ranar Laraba ya ce ya fice daga jam’iyyar ne saboda “rashin dimokuradiyyar cikin gida” da kuma zargin gazawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ba da damar kawo gyara a cikin jam’iyyar.

Jigon na APC ya sha sukar shugabannin jam’iyyar kan zargin karkatar da manufar kafa kasa da rashin rungumar garambawul.

Karin labari: Atiku ya jajantawa Shugaba Tinubu

Ya ce ya koma wani bangare ne domin hada kai da sauran shugabannin siyasa domin dorewar dimokuradiyya a kasar nan.

Ya ce, “Akwai yiwuwar ci gaba da kasancewa a APC idan har shugaban kasa Asiwaju Tinubu zai ba da damar yin gyara a cikin jam’iyyar don dawo da ita ga kafuwarta, wanda a matsayinta na mai nisa sosai.

“Saboda haka na canja sheka kuma zan yi kokarin yin aiki tare da duk ‘yan Najeriya masu kishin kasa wadanda suka amince da kuma bin manufar fafutukar tabbatar da wanzuwar dimokuradiyya da ci gaban dimokuradiyya a Najeriya.

Karin labari: KNUPDA: ‘Yan kasuwa 5,000 za su rasa shagunansu a jihar Kano

“Dole ne mu bunkasa dimokuradiyyar mu ta yadda zababbun wakilai a kowane mataki za su kasance masu bin jam’iyya kuma mai yiyuwa ne ‘yan Najeriya da ke da muradu daban-daban su kulla alaka mai karfi da jam’iyyun siyasa da zababbun gwamnatocin da za a iya aiwatar da manufofin gwamnatoci don nuna fa’idar muradun ‘yan Najeriya.

“Ina da yakinin cewa dimokuradiyya mai karfi tare da jam’iyyun siyasa na iya yiwuwa a Najeriya. Ina kuma da yakinin cewa a rayuwarmu za mu iya samar da gwamnatocin da za su iya inganta rayuwar ‘yan Nijeriya da gaske.

“Ba na tsammanin shugabannin jam’iyyar za su amince da shawarar da na yanke. Na yi imanin cewa a karshe, za mu kasance da hadin kai da dukkan shugabannin jam’iyyar da sauran ‘yan Najeriya masu kishin ci gaban dimokuradiyyar Nijeriya” in ji Mohammed.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here