Atiku ya jajantawa Shugaba Tinubu

Atiku, Tinubu, jajantawa, Shugaba
Dan takarar da shugaba Tinubu ya kayar a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, ya ce yana jajantawa Bola Tinubu dangane da zamewar da ya yi, a ranar...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Dan takarar da shugaba Tinubu ya kayar a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, ya ce yana jajantawa Bola Tinubu dangane da zamewar da ya yi, a ranar Laraba.

“Ina matukar jajantawa shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya samu a lokacin da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti na bikin ranar dimokuraɗiyya.

Karin labari: Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu ya fadi a filin bikin ranar Dimokuradiyya

“Ina fatan dai lafiya lau” in ji Atiku.

A baya-bayan nan dai an ga yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ke ƙara ƙaimi wajen yin hamayya ta fuskar sukan abubuwan da yake ganin gwamnatin shugaba Tinubu ba ta yi daidai ba, kamar yadda jaridar BBC Hausa ta bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here