Sanatoci uku sun fice daga PDP zuwa APC

Senate 1 750x430

Sanatoci uku daga jam’iyyar adawa ta PDP sun sauya sheka zuwa jam’iyyar (APC) mai mulki.

Sanatocin uku da suka sauya sheka dukkansu ‘yan jihar Kebbi ne, da suka hadar da Adamu Aliero, mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Yahaya Abdullahi, mai wakiltar Kebbi ta Arewa, da Garba Maidoki, mai wakiltar Kebbi ta Kudu.

Mutanen uku sun bayyana ficewarsu ne a wasu wasiku daban-daban da suka aike wa majalisar dattijai kuma mataimakin shugaban majalisar, Barau Jibrin, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya karanta a zaman majalisar na ranar Talata.

Kowanne daga cikin ‘yan majalisar ya bayar da misali da rikicin shugabanci da aka dade a cikin jam’iyyar PDP, wanda ke da nasaba da shari’o’in da ba a warware ba, da kuma rarrabuwar kawuna a cikin gida, a matsayin babban dalilin da ya sa suka yanke shawarar sauya sheka.

Idan dai za a iya tunawa, a baya dai Sanatocin uku sun gana da shugaban kasa Bola Tinubu a bayan fage a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Juma’a.

Karin karatu: PDP ta nada Ibrahim Shekarau a matsayin mamba a kwamitin Amintattu

Sun samu rakiyar shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris, gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu, da ministan kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki, Atiku Bagudu.

Duk da cewa ba a bayyana makasudin taron ba a lokacin, amma yanzu an tabbatar da cewa ya ta’allaka ne kan kammala shirinsu na komawa jam’iyyar APC.

A lokacin sauya shekar da aka yi a majalisar dattawan, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da suka hada da Dr. Abdullahi Ganduje, Nasir Idris, da karamin minista a ma’aikatar jin kai, Tanko Yusuf, sun hallara domin tarbar ‘yan majalisar.

Bayan karanta wasikar, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya taya ‘yan majalisar dattawan murna kan matakin da suka dauka na yin daidai da manufar jam’iyya mai mulki.

Daga nan ne kuma Messrs Aliero, Abdullahi da Maidoki suka yi musayar ra’ayi da sauran Sanatocin APC kafin a kai su sabbin kujerunsu a bangaren masu rinjaye na majalisar.

Yanzu haka akwai Sanatoci 107 a Majalisar Dattawa tun bayan rasuwar tsohon Sanatan Anambra ta Kudu, Ifeanyi Ubah, wanda ya rasu a watan Yulin da ya gabata, da kuma tafiyar Monday Okpebolo, wanda ya bar kujerar Edo ta tsakiya bayan an zabe shi Gwamnan Jihar Edo a watan Satumban da ya gabata.

Sanatocin uku da suka sauya sheka, ya haifar da yawan Sanatoci daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa 68.

A halin yanzu dai (PDP) tana da Sanatoci 30. Jam’iyyar Labour tana da Sanatoci biyar. Jam’iyyar (SDP) tana da Sanatoci biyu. NNPP tana da sanata daya, ita ma jam’iyyar (APGA) tana da daya.

Karin bayani daga baya…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here