Zulum yayi Allah wadai da hare-haren ISWAP da Boko Haram

IMG 20240429 WA0006 750x430

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya yi Allah wadai da hare-haren Boko Haram da ISWAP a wasu sassan jihar da suka hada da hanyar Maiduguri zuwa Damboa, Marte, Chibok, Gwoza, Kala Balge, da sauran al’ummomin da abin ya shafa.

Zulum, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Dauda Iliya, ya fitar ranar Talata a Maiduguri, ya jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya shafa, ciki har da wani abu mai fashewa da ta faru a ranar 12 ga watan Mayu a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa.

“Harin na IED ya yi sanadin mutuwar wasu ma’aikatan karamar hukumar Damboa guda biyu da aka ruwaito suna kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri domin zana jarabawar majalisar malamai ta kasa (TRCN).

“Sauran wadanda suka jikkata sun hada da sojoji da fararen hula da suka rasa rayukansu a wani tashin hankali da ya sake barkewa a jihar.

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na tallafawa gwamnatin tarayya, sojojin Najeriya, da sauran hukumomin tsaro a kokarin da ake na magance matsalar rashin tsaro a yankin.

Karin karatu: Gwamnonin Arewa na taro kan matsalar tsaro a Kaduna

Zulum ya kammala da mika addu’a ga iyalan wadanda suka mutu, wadanda suka jikkata, da dukkan ‘yan kasar da harin ya shafa. (NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here