Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na hukumar ilimi mai zirfi, Sunusi Kofar Na’Isa ya fitar ranar juma’a.
Sanarwar ta ce kwamishinan ilimi mai zirfi, Dr. Yusuf Kofar mata ne ya bayyanawa shugaban jami’ar bayeron hakan, farfesa Sagir Abbas a ofis din sa ya yin wata ziyara da kwamshinan ya kai masa.
Sanarwara ta kara da cewa kwamishinan ya bayyanawa shugaban jami’ar dalilin ziyarar tasa, inda ya ce yaje ne domin kara karfafa alakar gwamnatin kano da kuma jami’ar, sanan kuma su tau-tau na batun karin kudin makaranta da jami’ara tayi.
“Munzo gurinka ne dan mu hada karfi da karfi da hukumar BUK, kan batun karin kudi makaranta da akai, saboda mafiya yawan dalibai bazasu iya biyan wannan kudin ba.”
A nasa bangaren shugaban jami’ar ya yi maraba da zuwan kwamishinan, kuma ya bayyana mukamin da aka bashi na kwamishina a matsayin abinda ya dace.
“Muna kashe naira miliyan 100 a kowa ne wata domin aiyukan gudanar da jami’ar, haka kuma jami’ar buk tana kawai karbar kudin gudanarwa ne a gurin dalibai ba wai kudin makaranta suke biya ba.” Inji shugaban













































