Ana cikin fargaba a tsakanin shugabannin siyasa da na rundunar soji a Najeriya bayan rahotanni sun nuna cewa ana zargin wani yunkurin juyin mulki da ake cewa na iya zama barazana ga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu.
Rahotanni sun nuna cewa ana gudanar da bincike kan wasu jami’an soja da kuma fitattun ’yan siyasa daga yankunan kudanci da arewacin ƙasar da ake zargi da hannu a cikin lamarin.
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar a baya-bayan nan da kama jami’an soja 16 bisa abin da ta kira “tauye ƙa’idar aikin soja,” sai dai majiyoyi daban-daban sun bayyana cewa wannan kama na iya kasancewa da nasaba da binciken zargin shirya tada hankali a lokacin bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai na ƙasar nan a wannan watan.
Daga cikin waɗanda aka tsare akwai jami’an soja masu manyan mukamai a muhimman wurare na tsaro.
Hukumar leƙen asirin soja ta ƙasa (DIA) ce ke jagorantar binciken, tare da haɗin gwiwar rassan rundunar sojoji uku na ƙasar.
Ana kuma zargin cewa binciken ya wuce na jami’an soja kaɗai, har ya shafi wasu ’yan siyasa da ake zargin suna da hannu a lamarin.
Rahotanni daga kamfanin PRNigeria sun nuna cewa wani babban ɗan siyasa daga kudancin ƙasar yana ƙarƙashin bincike bisa zargin tallafawa wannan yunkuri.
Wasu daga cikin waɗanda ake binciken kuma ana zargin suna da alaƙa da gidajen sarauta da manyan iyalan siyasa, abin da ya haifar da fargaba game da girman wannan zargi.
Ko da yake ba a gurfanar da kowa a kotu ba tukuna, majiyoyi sun tabbatar cewa ana ci gaba da sa ido da kuma yi musu tambayoyi domin gano matsayin kowane ɗaya cikin shirin.
A halin yanzu hukumomin tsaro suna cikin shirin ko-ta-kwana domin tabbatar da tsaron ƙasa, sai dai wasu rahotanni sun nuna cewa babu wata hujja ta ƙwarai da ke tabbatar da zargin, domin babu wata kafar labarai ta ƙasashen waje da ta tabbatar da wannan batu kai tsaye, abin da ya haifar da shakku kan gaskiyar lamarin.
Majiyoyin tsaro sun ce wasu daga cikin jami’an da ake tambaya na iya kasancewa suna fuskantar bincike ne kan batutuwan cikin gida irin su matsalolin karin girma da halin walwala, amma aka haɗa lamarin da jita-jitar juyin mulki ba tare da hujja ba.
Har yanzu babu wata sanarwa ta hukuma daga gwamnati ko rundunar sojoji da ta tabbatar da zargin juyin mulkin. Saboda haka ana ganin wannan batu a matsayin abin da bai tabbata ba, kuma ake buƙatar a yi taka-tsantsan wajen yarda da shi.










































