Hatsari Ya Ritsa Ya Tawagar Motoccin Shahararren Gwamnan Arewa A Hanyar Zuwa Kamfe, Yan Majalisa Sun Jikkata 

c3fe2045e7d2dd0f
c3fe2045e7d2dd0f

Tawagar motoccin Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ta yi hatsari da garin Utokon da ke karamar hukumar Ado na jihar a ranar Juma’a.

Ortom da tawagarsa na hanyarsu na zuwa kamfen din dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a Igumale, hedkwatar Ado, ne a lokacin da abin bakin cikin ya faru.

Daily Trust ta rahoto cewa motar ta kubce wa direban motan da ke makil da magoya bayan PDP ya buga wa wata Jeep, wata motar jami’an tsaro da wata bas cikin tawagar gwamnan.

Motoccin da ke cikin tawagar sun hada da na mataimakin gwamnan jihar, Injiya Benson Abounu, Sanata Abba Moro, Mambobin majalisar wakilai na tarayya da yan majalisar dokokin jihar Benue, da wasu manyan jami’an gwamnati da jam’iyyar PDP a jihar.

Amma, ba da dadewa ba motar asibiti na gwamnatin jihar ta isa wurin da abin ya faru ta kwashe wadanda abin ya shafa ta tafi da su asibiti don yi musu magani.

Dakaci karin bayani …

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here