Shugaba Bola Tinubu ya bayar da lambar girmamawa ta Kwamandan Tarayyar Najeriya CFR ga hamshakin attajirin nan wanda ya kafa kamfanin Microsoft, Bill Gates.
Mai magana da yawun shugaban kasan, Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Facebook a yau Talata.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Lagos a daren ranar Talata ya ba da lambar yabo ta kasa ga hamshakin attajirin nan Bill Gates, wanda ya kafa Microsoft kuma wanda ya kafa gidauniyar Bill And Melinda Gates,” A cewar sanarwar Onanuga.
Shaidar karramawar ta CFR na ɗaya daga cikin mafi girman karramawa a Najeriya da ake bai wa daidaikun mutane don girmamawa ta musamman.
Gates, Shugaban Gidauniyar Bill & Melinda Gates, a halin yanzu ya na ziyarar aiki ne a Afirka, inda ya sauka a Habasha da Najeriya.










































