Jawabin Tinubu a takaice a bikin Najeriya @64

Bola Tinubu Tinubu 750x430

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba wa ’yan Najeriya haƙuri game da halin tsadar rayuwa da yunwa da rashin aikin yi da suke fama da su.
Ya kuma ba su haƙuri game da tsare-tsaren da gwamnatinsa ta bullo da su, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen kawo tsadar rayuwa da yunwa a Najeriya, yana mai cewa nan gaba ’yan ƙasar za su dara.

Ya ce, “ina ba ku tabbacin cewa abinci zai wadata kuma ya yi sauki a ƙasar nan. Wannan alƙawari na yi muku, kuma ba zan saɓa ba.”

A cewarsa, “a sakamon tsare-tsaren da gwamnatinmu ta yi, a shekarar da ta gabata ’yan kasashen waje sun zuba jari na Dala biliyan 30 a Najeriya.”

Ya ci gaba da cewa, “duk cewa tsadar rayuwa matsala ce da ta shafi duniya, amma za mu yi mai yiwuwa wajen ganin farashi ya sauka a cikin gida.”

A jawabinsa na zagayowar Ranar Samun ’Yancin Najeriya karo na 64, Tinubu ya shaida musu cewa yana sane da halin da suke ciki, kuma zai ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen magance matsalolin da suka dabaibaye ƙasar.

Ya ce duk da matsalolin da gwamnatinsa mai watanni 16 a bisa mulki ta gada, tana kan yin ƙoƙari don tabbatar da ganin al’amura sun kyautatu a ƙasar.

A cewarsa, “Na karɓi mulki a yanayi na matsalar tsaro da tattalin arziƙi kuma ba mu da zabi face yin sauye-sauye domin samun cigaba ko kuma mu ci gaba da abin da muka tarar a ƙarshe ƙasar ta durƙushe.

“Amma sai muka zaɓi yin gyare-gyare a fannin tattalin arziƙi da tsaro, inda muka ragargaji mayaƙan Boko Haram da ’yan ta’adda har aka samu sauƙi a yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.”

Ga wasu muhimman abubuwa a taƙaice daga jawabin shugaban ƙasan.

Jawabin Tinubu a taƙaice:

1. Na san halin matsin rayuwa da rashin aiki da kuke ciki, don haka ina ba ku haƙuri da tabbacin magance su don ku samu sa’ida.

2. Ku yi haƙuri da tsare-tsaren gwamnatinmu domin kyawawa ne kuma an fara ganin amfaninsu.

3. A tsawon shekarun da Najeriya ta yi da samun ’yanci mun cimma wasu burikan waɗanda suka yi fafutikar samun ’yancin.

4. ’Yan Najeriya sun zama abin koyi da alfahari a fannoni daban-daban na rayuwa a faɗin duniya, kuma kullum ƙaruwa suke yi.

5. Mun ɗauki darasi daga wasu kura-kuranmu na baya inda muka ci gaba da ɗorewa a matsayin ƙasa ɗaya dunƙulalliya, duk da yaƙin basasa da sauran rikice-rikice da bambance-bambance da matsalolin da muka yi ta fama da su a tsawon shekaru 64.

6. Na karɓi mulki a yanayi na matsalar tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziƙi kuma ba mu da zaɓi face yin gyare-gyare don samun cigaba ko kuma mu ɗora a kan abin da muka tarar a ƙarshe ƙasar ta durƙushe, ina muka zaɓi na farko, muka inganta ɓangaren tattalin arziki da na tsaro.

7. Manufarmu ita ce kawar da ta’addancin ’yan bindiga da masu tsattsuran ra’ayi inda cikin shekara guda muka hallaka gaggawa shugabannin Boko Haram da ’yan fashin daji 300 a yanikn Arewa da sauran sassan Najeriya.

8. Aminci ya samu a daruruwan yankuna inda ’yan gudun hijira suka koma gidajensu kuma za mu ci gaba da hakan har sai dukkansu sun koma garuruwansu an ci gaba da harkokin noma domin samun wadatar abinci a ƙasa.

9. Mun jajanta tare da tallafa wa mutanen Maiduguri da ambaliya ta shafa, muka sa a yi wa duk madatsun ruwa da ke ƙasar nan gwajin domin kauce wa lalacewarsu da ambaliya sannan majalisar zartarwa amince da Gidauniyar Tallafin Gaggawa domin ba da damar kai ɗauki a lokacin ibtila’i.

10. Sakamon tsare-tsaren da gwamnatinmu ta yi, a shekarar da ta gabata ’yan ƙasashen waje sun zuba jari na Dala biliyan 30 a Najeriya

11. Za mu sauƙaƙa hanyoyin gudanar da kasuwanci cikin doka.

12. Nan ba da jimawa ba za mu sa sannu kan takardar izini ga kamfanin ExxonMobil Seplat domin gudanar da harkoki a ɓangaren ɗanyen mai domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar nan.

13. A watan Agusta mun biya bashin ƙasashen waje na Dala biliyan bakwai daga cikin Dala biliyan 30 da muka gada, sakamakon sabbin tsare-tsaren Babban Bankin Najeriya (CBN) na farfaɗo da darajar Naira.

14. Mun rage yawan cin bashin ƙasashen waje daga kashi 97% zuwa 68% kuma muna ci gaba da tsare-tsaren samar da ayyukan yi da gudanar da sana’o’i cikin sauki.

16. Mun tabbatar da dokar ’yancin ƙananan hukumomi.
17. Jinjina gwamnonin  Kebbi, Niger, Jigawa, Kwara, Nasarawa, da sauransu da suka rungumi harkar noma kuja muna kira ga sauran da su rungumi shirin Gwamnatin Tarayya na na noman zamani.

18. Za mu samar da takin zamani da takarktoci 2,000 da sauran motoci da injina da kayan aikin noma nan da watanni shiga masu zuwa.

19. Za mu taimaka wa jihohi wajen sayen motoci masu amfani da gas ɗin CNG domin sauƙaƙe tsadar sufuri ga al’umma.

20. Za mu ci gaba ayyukan haɗa kan al’ummar ƙasa domin sai da zaman lafiya za a samu cigaban da ake buƙata.

21. Lura da muhimmancin matsa, waɗanda su ne kashi 60 na al’ummar Najeriya wajen gina ƙasa da rayuwar nan gana, mun shirya taron matasa ma ƙasa na kwana 30, domin tattaunawa da su kan ainihin buƙatunsu da matsalolinsu don magance su ta hanyar ɗaukar matakai da ɓullo da tsare-tsaren da suka dace.

22. Hakazalika akwai shirin 3MTT na sama wa matasa miliyan uku ƙwarewa a fannonin fasahar zamani da ke gudana a halin yanzu.

22. Akwai kuma shirin tallafin karatun dalibai  (NELFUND) da shirin tallafin dogaro da kai (LEEP) ga matasa miliyan 2.5 a shekara.

22. An ba wa Shugabar Alƙalan Najeriya da a Shugaban Majalisar Dattawa lambar girmawa ta (GCON). Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da Shugaban Majalisar Wakilai kuma lambar (CFR), mataimakinsa kuma lambar (CON).

22. Nan gaba za a sanar da jerin sunayen sauran waɗanda suka samu lambobin girmamawan.

23. Kada ku yanke ƙauna daga yiyuwar cire kitse daga wuta domin kyautata rayuwar al’ummar ƙasar nan da cikar burinsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here