Tsohon shugaban NLC Ciroma ya rasu

Comrade Ali Ciroma, shugaban, kungiyar, NLC
Sakataren kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, Ali Ibrahim Ciroma, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce marigayi shugaban kwadagon ya rasu ne a asibitin koyarwa...

Sakataren kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, Ali Ibrahim Ciroma, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce marigayi shugaban kwadagon ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno a ranar Talata.

Sakataren NUJ kuma dan uwa ne na kungiyar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A cikin alhini na sanar da rasuwar Kwamared Ali Ciroma, tsohon shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya.

Karin labari: Kungiyar NCAC ta shawarci shugaba Tinubu kan mayar da Betta Edu matsayinta

“Lamarin ya faru ne da yammacin ranar talatar da ta gabata 2 ga watan Afrilu a asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri.

“Wanda a ranar Larabar nan ake sa ran yin jana’izar mamacin da karfe 4 na yamma a gidansa mai lamba 7A kan titin Galadima kusa da asibitin tunawa da Muhammadu Shuwa (Gidan jinya), Maiduguri.”

Karin labari: Yanzu-yanzu: Majalisar dokokin Kano ta tantance Mustapha Kwankwaso

Ciroma ya kasance shugaban NLC daga 1984 zuwa 1988 a lokacin da gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Babangida ta tilasta masa yin murabus, wanda ya rusa kungiyar.

Gwamnatin Abacha ta dawo da shi cikin hadin kai, inda ta nada shi a matsayin shugaban kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya tilo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here