Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya Mora ya rasu

Juan Vicente Perez Mora, duniya, rasu, tsufa
Juan Vicente Perez Mora dan kasar Venezuela, wanda Guinness World Records ya tabbatar a shekarar 2022 a matsayin mutum mafi tsufa a duniya, ya mutu ranar...

Juan Vicente Perez Mora dan kasar Venezuela, wanda Guinness World Records ya tabbatar a shekarar 2022 a matsayin mutum mafi tsufa a duniya, ya mutu ranar Talata yana da shekaru 114, in ji jami’ai da dangi.

“Juan Vicente Perez Mora ya rasu ne yana da shekaru 114,” in ji shugaban Venezuela Nicolas Maduro a dandalin sada zumunta na X.

An tabbatar da Perez a matsayin mutum mafi tsufa a duniya a ranar 4 ga watan Fabrairu, 2022, lokacin yana da shekaru 112 da kwanaki 253, a cewar Guinness.

Karin labari: Tsohon shugaban NLC Ciroma ya rasu

An bayyana yana da ‘ya’ya da jikoki da dama.

An haifi manomin da aka fi sani da Tio Vicente a garin El Cobre, a jihar Tachira ta Andean a ranar 27 ga watan Mayu, 1909, kuma shi ne na tara a cikin yara 10.

Karin labari: Kungiyar NCAC ta shawarci shugaba Tinubu kan mayar da Betta Edu matsayinta

“A lokacin yana dan shekara biyar, ya fara aiki tare da mahaifinsa da ‘yan uwansa a harkar noma kuma ya taimaka da rake da kuma girbin kofi,” in ji sanarwar Guinness daga 2022.

Perez ya ci gaba da zama sheriff kuma yana da alhakin warware filaye da rikice-rikice na iyali, yayin da yake aiki a aikin gona.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here