A yau Talata ne tawagar ƴan wasan Najeriya na Super Falcons ta ta lallasa Lionesses ta ƙasar Kamaru da ci 2-0 a wasan sada zumunta da suka buga a filin wasa na MKO Abiola da ke Abeokuta.
Kyaftin Rasheedat Ajibade ce ta fara cin kwallo a minti na 28 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Haka kuma, a minti na 43 ne Ajibade ta sake zura kwallo ta hannun Babajide Omorinsola ta bangaren Hagu.
‘Yan wasan Kamaru sun fafata sosai a zagaye na biyu amma gwarazan ‘yan wasa biyu Payne Antoinette da Isah Sikiratu suka hana su ci.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala wasan, mai horas da ƴan wasan Super Falcons Justin Madugu ya yaba wa ‘yan wasan saboda kwazon da suka nuna.
Madugu ya ce har yanzu kungiyar ta na da sauran aiki a gabanta, inda ya ƙara da cewa, zakunan sun kasance tawaga tagari.













































