Jami’ar jihar Kwara (KWASU) Melete, ta ce dakatarwar shekara daya da aka yi na bada gurbin karatu ga daliban shari’a a baya bayan nan ba zai shafi daliban da yanzu haka suke karatu a tsangayar koyar da harkokin shari’a ba.
Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na jami’ar Dr Saeedat Aliyu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Alhamis din nan a Ilorin.
Dakta Aliyu, ya ce dakatarwar ta biyo bayan matakin da majalisar kula da harkokin ilimin shari’a ta dauka na sanyawa KWASU takunkumi kan fara shirin bada horon ilimin harkokin shari’a a shekarar 2018 bisa amincewar hukumar kula da jami’o’I ta kasa (NUC) kadai.
A cewarsa, a halin yanzu jami’ar KWASU ta samu cikakkiyar amincewa daga hukumar NUC da majalisar CLE don gudanar da tsarin karatun digiri na biyu, da harkokin shair’a da kuma na shari’ar Musulunci.
“Hukumar gudanarwar jami’ar na sanar da cewa dakatarwar ta shekara 1 bata shafi daliban da suke gudanar da karatu yanzu haka a tsangayar shari’ar ba”.
labarai mai alaka da wannan: Jami’ar KHAIRUN ta jaddada kudirinta na bada ilimi mai inganci cikin sauki ga sabbin dalibanta da sauran dalibai
“jamia’ar KWASU za ta ci gaba da kasancewa mai yin biyayya ga dukkanin hukumomin ilimi, da kuma tukunkumin da majalisar CLE ta sanya, ta hanyar baiwa dalibai guraban karatu a zango na shekarar 2025/2026” a cewar Dakta Aliyu.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa, hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan JAMB ta sanar da cewa ba za ta gudanar da jarrabawar ba a jami’ar KWASU da wasu jami’o’i Bakwai ba a fadin kasar nan.
Hakan ya biyo bayan dakatar da shirin karatun digiri na biyu da majalisar CLE ta yi na zangon karatun 2025/2026 a jami’o’in da abin ya shafa.













































