Mataimakin Daraktan REMASAB ya mayar da naira miliyan 4.7 da aka biya shi bisa kuskure

Screenshot 20250130 124033 WhatsApp

Mataimakin Daraktan Kwashe Shara da Kuma Tsabtar Muhalli ta Jihar Kano (REMASAB), Lamir Mukhtar Hassan, ya mayar da sama da naira miliyan 4.7 ga gwamnatin jiha bayan gano cewa an biya shi kudin ne bisa kuskure a matsayin biyan bashin albashi sau biyu.

Hassan ya bayyana cewa an biya shi bashin albashinsa na naira 4,700,861.55 a watan Disamba na shekarar 2024.

Sai dai a watan Janairu, ya gano cewa an sake tura masa adadin kudin da aka riga aka biya shi, lamarin da ya ba shi mamaki.

SolaceBase ta ruwaito cewa Hassan yana fahimtar kuskuren da aka yi ya gaggauta mayar da kudin zuwa asusun ajiyar gwamnati a ranar Litinin.

Wannan dabi’a ta gaskiya ta samu yabo daga jama’a, inda da dama suka jinjinawa Hassan bisa kyakkyawar amanarsa a wannan lokaci na matsin tattalin arziki.

 

A wata tattaunawa da SolaceBase, Hassan ya ce, “Ba kudina ba ne, don haka ba ni da hakkin riƙe su. Kudadene na al’ummar Jihar Kano. Na mayar da su domin gwamnati ta ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba.”

Yayin da yake bayanin lamarin, Hassan ya ce, “Lokacin da Gwamna Yusuf ya naɗa ni, na fuskanci matsalar albashi har zuwa watan Oktoba.

“An biya ni bashin albashin a watan Disamba, amma a ranar 27 ga watan Janairu, na sake ganin an turo min kudin a karo na biyu, wanda na san kuskure ne,” in ji shi.

Bayan lura da ƙarin kashi 85 cikin 100 a albashinsa, Hassan ya tabbatar cewa an yi kuskure, don haka ya yanke shawarar mayar da kudin.

Ya nuna wa SolaceBase takardu da bayanan banki da ke tabbatar da cewa an mayar da kudin ga gwamnatin jiha.

Hassan ya kuma yi kira ga ma’aikatan gwamnati da al’umma gaba ɗaya da su kasance masu gaskiya da rikon amana a harkokinsu.

“Mu yi iyakar kokarinmu wajen riƙe gaskiya kuma mu guji karɓar abin da ba na mu ba,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here