CAC Ta Gano Kamfanoni 189 Na Bogi

CAC
CAC

Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci (CAC) ta ce ta gano wasu kamfanoni na bogi 189 da aka yi amfani da su wajen tabbatar da rabon filaye a Babban Birnin Tarayya .

Babban magatakardar hukumar, Hussaini Magaji ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Talata a Abuja.

Magaji ya bayyana cewa an gano hakan ne biyo bayan korafin da hukumar babban birnin tarayya ta yi na tabbatar da halin da wani kamfani da ba shi da shi ke neman rabon fili.

Ya bayyana cewa, gano kamfanin da babu shi ya sa ya kara yin bincike, wanda ya sa aka gano wasu kamfanoni.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here