Ganduje ya yi kira da a samar da wasu ayyuka na musamman a tsarin mulki ga mataimakan gwamnoni a Najeriya

ganduje, kotu, APC, dakatar, tabbatar
Wata babbar kotu a jihar Kano ta dakatar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ga shugabancin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.Mai shari'a Usman Malam...

Dr Abdullahi Ganduje, shugaban jam’iyyar APC ta kasa, ya yi kira da a samar da wasu ayyuka na musamman na tsarin mulki ga mataimakan gwamnoni a Najeriya domin su shagaltu da su.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a taron shekara-shekara na kungiyar Tsoffin Mataimakan Gwamnonin Najeriya (FFDGN) mai taken: “Hadin kai a cikin manufa daya don samar da shugabanci na gari da ci gaba mai dorewa” a Abuja.

Gwamna Ganduje, wanda ya samu wakilcin Mista Emma Eneukwu, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, na Kudu, ya bayyana cewa bayar da ayyukan da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada zai hana a samu rikici tsakanin gwamnoni da mataimakansu.

Shima da yake magana tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Cif Kanu Agabi ya shawarci shugabannin siyasa da su kasance masu kishin kasa su jagorance su a duk harkokinsu.

Ya ce babu laifi a kundin tsarin mulkin Najeriya, illa rashin kiyaye shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here