2027: INEC ta musanta fitar da jadawalin babban zaɓe

INEC 1 1 750x388

Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a wasu sassa na ƙasar da ke cewa ta fitar da jadawalin da tsarin ayyuka na babban zaɓen shekarar 2027, inda ta bayyana bayanan a matsayin ƙarya da ruɗani.

Hukumar ta bayyana cewa ba ta fitar da wani jadawalin zaɓe ko tsarin ayyuka na zaɓen 2027 ba, duk da cewa a baya ta gabatar da wasu hasashe a cikin wani littafi mai taken Election Management in Nigeria, 2015–2025, wanda ya kunshi bayanan ayyukan da aka gudanar a shekaru goma da suka gabata.

INEC ta tuna cewa a ƙarshen wa’adin shugabancin Farfesa Mahmood Yakubu, hukumar ta gabatar da littattafai guda biyu ga jama’a, inda ɗaya ya mayar da hankali kan gudanar da zaɓe tsakanin 2015 zuwa 2025, yayin da ɗayan ya tattauna sabbin fasahohin da aka shigar wajen gudanar da zaɓe a wannan lokaci.

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai kuma mai ba shugaban INEC shawara kan harkokin yaɗa labarai, Adedayo Oketola, ya sanya wa hannu a Abuja, hukumar ta jaddada cewa babu wani jadawali ko tsarin ayyuka da aka fitar dangane da babban zaɓen 2027.

Hukumar ta kuma yi bayani cewa tsohon shugaban INEC ya daura manyan zaɓukan ƙasa a kan tsarin dindindin, inda zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokoki ke gudana a duk ranar Asabar ta uku ta watan Fabrairu, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi ke zuwa bayan makonni biyu.

Duk da haka, INEC ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za ta fitar da cikakken jadawalin da tsarin ayyuka na babban zaɓen 2027 a kan lokaci, bisa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasa da kuma dokar zaɓe ta shekarar 2022, tare da isar da bayanai ta hanyoyin ta na hukuma da aka tabbatar.

Hukumar ta yi kira ga jama’a da kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da rahotannin bogi, su kuma dogara kacokan ga bayanan da ke fitowa daga kafafen INEC na hukuma domin samun sahihanci da ingantaccen bayani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here