Babbar kotun jihar Kano ta bayar da umarnin wucin gadi na dakatar da Hashimu Suleiman-Dungurawa daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, har sai an yanke hukunci a kan karar da ke gaban kotu.
Suleiman-Dungurawa dan mazabar Gargari ne da ke karamar hukumar Dawakin-Tofa a jihar Kano, inda rikicin shugabancin jam’iyyar ya samo asali daga wannan mazaba.
Mai shari’a Zuwaira Yusuf ce ta bayar da umarnin, bayan gabatar da bukatar gaggawa daga Shuaibu Hassan tare da wasu mutum tara, dukkansu mambobin jam’iyyar NNPP na mazabar Gargari a karamar hukumar Dawakin-Tofa.
Wadanda ake kara a shari’ar su ne Suleiman-Dungurawa da jam’iyyar NNPP, inda kotu ta duba bukatar tabbatar da matakin ladabtarwa da jam’iyyar ta dauka a kansa.
Karanta: A Gaggauce: NNPP ta kori shugaban jam’iyyar na Kano, Dungurawa makonni biyu bayan sake zaɓensa
Kafin wannan umarni na kotu, shugabannin zartarwa 27 na jam’iyyar a matakin jiha sun yanke shawarar dakatar da Suleiman-Dungurawa daga mukaminsa a ranar 30 ga Disamba, bisa wasu zarge-zarge da aka alakanta da shi.
Masu shigar da karar sun bukaci kotu ta tantance ko matakin da aka dauka ya yi daidai da kundin tsarin jam’iyyar NNPP, musamman kan zargin cin mutuncin ofishin gwamnan jihar Abba Kabir-Yusuf, haddasa rabuwar kai a cikin jam’iyya, da kuma gaza biyan kudaden jam’iyya.
Kotun ta umarci Suleiman-Dungurawa da ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban NNPP na Kano, tare da tabbatar da cewa dakatarwar za ta ci gaba har zuwa sauraron karar a ranar 19 ga Janairu.
Tuni dai jam’iyyar ta amince da nadin Abdullahi Zubairu-Abiya a matsayin mukaddashin shugaban NNPP na Kano, kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanada.
NAN













































