Yanzu-yanzu:Kungiyoyin NLC da TUC sun ayyana tafiya yajin aiki a fadin kasar nan daga mako mai zuwa

Ajaero 600x430
Ajaero 600x430

Gamayyar kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun ayyana tafiya yajin aiki a fadin kasar nan daga ranar Talata 14 ga watan da muke na Nuwamba.

Daukar matakin ya biyo bayan taron kwamitin zartarwa na kungiyoyin wanda sakataren kungiyar NLC na kasa Emanuel Ugboaja da shugaban kungiyar TUC Festus Osifo suka jagoranta a Abuja.

Tun da farko a yayin taron, kungiyoyin kwadagon sun sake tattauna batun yajin aikin da suka shirya yi biyo bayan dukan shugaban kungiyar NLC na kasa, Joe Ajaero da jami’an tsaro suka yi.

A baya dai Kungiyoyin sun bada wa’adin kwanaki biyar ne cewa za su shiga yajin aiki a fadin kasar nan, biyo bayan kama Ajaero da jami’an tsaro suka yi a birnin Owerri na jihar Imo.

An dai kama Ajaero ne tun a ranar Laraba 1 ga watan Nuwambar shekarar da muke ciki ta 2023, yayin da ma’aikata ke tsaka da gudanar da zanga-zanga a fadin jihar Imo, sakamakon kin biyansu albashin su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here