Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da nada sabuwar Hukumar Gudanarwar Kano Pillars

Gwamnan, Kano, Abba, Kabir, Yusuf, amince, nada, sabuwar, Hukumar, Gudanarwar, Kano, Pillars
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin sabuwar gudanarwa ta kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars. Nadin na zuwa ne bisa la'akari...

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin sabuwar gudanarwa ta kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Nadin na zuwa ne bisa la’akari da wa’adi da rusa kwamitin gudanarwar kungiyar kwallon kafar.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.

A cewar sanarwar an zabo sabbin mambobin hukumar cikin tsanaki don kwarewa da gogewar su kuma za su yi aiki na wucin gadi na shekara guda, tare da yiwuwar sabunta su bisa la’akari da kwazon kungiyar a yanayi mai zuwa.

Karin labari: Kenneth Okonkwo ya fice daga jam’iyyar LP tare da sukar Peter Obi

SolaceBase ta bayyana cewa sabuwar hukumar ta ƙunshi Ali Muhammad Umar (Nayara Mai Samba) – Shugaba da Salisu Kosawa – Honorary Mamba, da Yusuf Danladi (Andy Cole) – Mamba, da Nasiru Bello – Mamba, da Muhammad Ibrahim (Hassan West) – Mamba, da Muhammad Usman – Mamba, da kuma Muhammad Danjuma Gwarzo – Mamba, tare da Mustapha Usman Darma – Mamba, da kuma Umar Dankura a matsayin Mamba.

Sanarwar ta ce wasu sun hada da Ahmad Musbahu – Mamba, da Rabiu Abdullahi – Mamba, da kuma Abubakar Isah Dandago Yamalash – Daraktan yada labarai, har ma da Ismail Abba Tangalash – mataimakin daraktan yada labarai da Injiniya Usman Kofar Na’isa a matsayin Mamba.

Karin labari: An kashe Mutum 2 a harin da Boko Haram ta kaiwa ofishin ‘Yan Sanda a Borno

Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwar cewa wadannan mutane za su zo da dimbin ilimi da gogewa da za su taimaka wajen tafiyar da harkokin kungiyar ta Kano Pillars FC.

Ana sa ran sabuwar hukumar za ta yi aiki kafada da kafada da ma’aikatar matasa da wasanni ta jiha da sauran masu ruwa da tsaki a harkar wasanni domin bunkasa kungiyar Kano Pillars.

Bugu da kari, gwamnan ya amince da nada Kyaftin din Super Eagles na Najeriya, Ahmed Musa a matsayin jakadan wasanni na jihar Kano.

Shigarsa ba kawai za ta zaburar da ‘yan wasan ba ne har ma da daukaka martabar kungiyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here