Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta cafke wata mata bisa zargin kashe mijinta a unguwar Pegi da ke Abuja.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba a Abuja.
Ta ce jami’an rundunar ‘yan sandan da ke aiki da sashin ‘yan sanda na Pegi, sun kama wanda ake zargin ne a ranar Talata da misalin karfe 6:00 na yamma, bayan samun bayanan sirri.
Adeh ta ce an kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake yunkurin guduwa da kayan mijin nata da aka ce ya bata kusan kwanaki uku.
Kakakin ‘yan sandan ya ce jami’an ‘yan sandan sun kama wanda ake zargin ne a cikin wata karamar mota.
“Da aka yi masa tambayoyi, wadda ake zargin ta amince da kashe mijinta bayan fada ya barke a tsakaninsu.
“Daga baya ta jagoranci ‘yan sandan zuwa wani gini da ba a kammala ba inda ta jefar da gawar da ta kone,” in ji ta.
A cewarta, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, kwamishinan ‘yan sanda (CP) mai kula da babban birnin tarayya Abuja, Mista Benneth Igweh, ya tabbatar da cewa za a yi adalci kan lamarin.
Adeh ya ce CP ya umarci mazauna babban birnin tarayya Abuja da su sanar da yan sandan duk wani rahoto da suka shafi ‘yan sanda ta hanyar lambobin GSM kamar haka: 08032003913, 08028940883, 08061581938 da 07057337653. (NAN)