Mazauna Kano sun kuka kan rashin sabis, sun nemi a kawo musu dauki

telecom mast4

Masu amfani da manyan layikan sadarwa a Kano sun koka da rashin kyawun sadarwar intanet da kiran waya a cikin birni.

Wadanda suka zanta da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a wata tattaunawa daban-daban a ranar Talata a Kano, sun ce lamarin ya jawo musu wahala da damuwa.

Moses Isiyaku, ya koka da yadda ya fuskanci matsalar intanet da sabis na kira kwanan nan.

A cewarsa, wannan yanayi mara dadi ya jawo wa ‘yan Najeriya wahalhalun da ba za a iya mantawa da su ba, saboda ya rasa wani muhimmin jirgin da zai tashi zuwa Legas saboda rashin ingancin sadarwar intanet da kiran waya.

Wani dan kasuwa, Abubakar Isah, ya ce a baya-bayan nan an samu matsala ta hanyar sadarwa.

Ya ce kamfanonin sadarwa a kasar nan ba su damu da halin da ake ciki ba.

Isah, wanda ya yabawa Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) bisa kokarinta na tsawon shekaru, ya bukace ta da ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kare masu layukan waya.

Ahmed Nuhu, shima ya ce tsarin sadarwa a kasar nan bai yi kyau ba a ‘yan kwanakin nan.

Sai dai ya yi kira ga hukumomin da su shiga cikin lamarin.

Ita ma wata malamar makaranta, Maryam Adamu, ta bukaci kamfanonin sadarwa da su inganta ayyukansu saboda ‘yan Najeriya sun fusata da su.

Ta kuma koka da yadda aka rufe ofishin MTN da ke cikin birni inda ta je dauko layinta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here