Sabon Hari: Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 5, Sun Kuma Yi Garkuwa Da Mutum 5 A Katsina

Nigeria Kidnappings Bandits deputy
Nigeria Kidnappings Bandits deputy

Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari a unguwar Sayaya da ke karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina, inda suka kashe akalla mutane biyar.

Lamarin wanda ya faru da sanyin safiyar Talata, ya zo ne sa’o’i 24 bayan harin da aka kai a taron Mauludin inda aka ce akalla mutane 25 ne suka mutu.

Matazu da Musawa dai na makwabtaka da kananan hukumomin inda wasu daga cikin wadanda harin taron Mauludin ya rutsa da su suka fito.

Wani mazaunin garin Sayaya, wanda ya ce mahaifinsa na cikin wadanda aka kashe, ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun kai farmaki gida-gida a cikin al’umma, inda suka kashe biyar tare da yin awon gaba da wasu da dama.

Ya ce ‘yan ta’addan sun kuma yi awon gaba da dabbobin su tare da kwashe wasu kayayyaki masu daraja a yayin farmakin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here