Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya bayyana alhini kan hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai ‘yan al’ummar Lawanti da ke karamar hukumar Akko a jihar.
Rahotanni sun nuna cewa mamatan na kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri a jihar Borno ne domin halartar bikin aure lokacin da hatsarin ya auku, lamarin da ya jefa iyalai da al’ummar yankin cikin jimami.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan lamari babban rashi ne mai radadi, ba ga iyalan da abin ya shafa kadai ba, har ma ga daukacin al’ummar Lawanti, karamar hukumar Akko da kuma jihar Gombe baki daya.
Ya jaddada cewa rasuwar rayuka a irin wannan yanayi ta taba zukatan jama’a matuka, inda ya nuna cewa ba kalmomi da za su wadatar wajen kwantar da hankalin iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a irin wannan mummunan lamari.
Gwamnan ya jajanta wa iyalan mamatan, ciki har da dagacin Jalingo, Bello Hassan Babangida, wanda ya rasa ‘yar uwarsa da ‘yar ‘yarta, da Idris Lawanti Maigari da ya rasa ‘yarsa, da kuma Idris A. Isah Lawanti, kansilan wakiltar mazabar Akko, wanda shima ya rasa makusanta.
Ya yi addu’ar Allah Ya ba iyalai da ‘yan uwa da daukacin al’ummar Lawanti hakuri da juriyar jure wannan babban rashi, Ya gafarta wa mamatan kura-kuransu, Ya karbi kyawawan ayyukansu, tare da sanya su cikin Aljannatul Firdaus.













































