Wani abin fashewa ta yi ƙara a jihar Kwara, bayan hare-haren jiragen sama na Amurka kan ‘yan ta’adda a Sokoto

Untitled 1 1813

Wasu abubuwan fashwewa da suka yi ƙara da tsakar dare sun jefa al’ummar Offa a jihar Kwara cikin firgici, inda suka lalata gine-gine da dama a wasu sassan garin.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a wurare biyu daban-daban, ciki har da filin Eid da kuma wani otel mai suna Solid Worth Hotel.

Mutanen da ke zaune a yankin sun bayyana cewa gine-gine fiye da biyar sun rushe gaba ɗaya sakamakon fashewar, kodayake babu tabbacin samun asarar rayuka a lokacin da lamarin ya faru. Bayan haka, an samu wata fashewa a kusa da filin Idi na Yidi da ke Offa, inda shima ya janyo mummunar lalacewa ga gine-gine a yankin.

Bincike ya nuna cewa ba a tabbatar da musabbabin fashewar ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto. Hukumomin tsaro sun killace wuraren da abin ya shafa tare da fara gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya haddasa fashewar.

Karin labari: Borno: Ƴar Ƙaunar baƙin Wake ta kashe mutane 24 a wajen sayar da abinci

Gwamnatin karamar hukumar Offa ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta samu rahotannin wani abu da ake zargin alaka da kayan fashewa a yankin filin sallar Yidi. Hukumomin tsaro sun dauki matakan tsaro tare da fara bincike, yayin da shugaban karamar hukumar ya kai ziyara wurin domin tantance halin da ake ciki.

Shugaban karamar hukumar ya bukaci al’umma su kwantar da hankalinsu, su kasance masu lura da tsaro tare da bin doka da oda, yana kuma shawartar jama’a da su rika dogaro da sahihan bayanai daga hukumomi domin kauce wa yada firgici.

Fashewar ta auku ne ‘yan awanni bayan Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da kai hare-haren jiragen sama kan wasu wuraren ‘yan ta’adda a jihar Sokoto, a wani bangare na yunkurin dakile ayyukan kungiyoyin masu tayar da kayar baya a arewa maso yammacin Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here