Borno: Ƴar Ƙaunar baƙin Wake ta kashe mutane 24 a wajen sayar da abinci

Car bomb blast in Kaduna, Nigeria
epa03175758 Nigerians look on at the damage after a suicide bomber detonated a car bomb in Kaduna, Nigeria 08 April 2012. Reports indicate two car bombs exploded in Kaduna in the north of Nigeria killing at least six and injuring several people. The blasts in a built up area next to a restaurant and church caused extensive damage. Hundreds of lives have been claimed in similar terror attacks in recent months due to religeous conflict. EPA/STR

Kimanin mutane 24 ne rahotanni suka ce sun mutu bayan wata ƴar ƙunar baƙin Wake ta kai hari a wani wurin cin abinci da ke karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Zagazola Makama, wani manazarci kuma mai bibiyar ayyukan yaƙi da ƴan tada ƙayar baya da ya mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi, ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar Juma’a, inda wasu da dama suka samu munanan raunika.

Shafin jaridar ta Zagazola Makaman, ta ruwaito cewa ƴar ƙunar baƙin waken ta tayar da Bam ɗin ne l a wurin dafa abinci.

Haka kuma ta ce, gawar ƴar ƙunar baƙin Waken ta tarwatse ne sakamakon fashewar Bam ɗin, inda aka tsinci kanta kawai.

Ya ce, an ajiye gawarwakin waɗanda suka mutu a ɗakin ajiyar gawarwaki, yayin da waɗanda suka jikkata aka kai su wani asibiti da ke kusa, inda suke karbar magani.

Tawagar tsaro ta hadin gwiwa wadda ta hada da sojoji da ‘yan sanda da rundunar hadin gwiwa ta farar hula ta CJTF, da mafarauta sun ziyarci wurin da tashin Bam din ya faru.

Sanarwar ta ce, tun daga lokacin an killace yankin yayin da aka tsaurara matakan tsaro a fadin Konduga domin hana kai hare-hare.

Har yanzu dai rundunar ƴan sandan jihar Borno ba ta ce uffan ba kan faruwar lamarin.

A watan Agustan shekarar 2024, aƙalla mutane 17 ne suka mutu bayan wani da ake zargin ɗan kunar bakin Wake ne ya kai hari a wata kasuwa a Konduga.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here