Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana cewa gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin gina jami’ar hulɗar jama’a da jagoranci ta farko a duniya gaba ɗaya daga ajiyar kuɗin da ta tara, ba tare da karɓar rance ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a Gudi da ke karamar hukumar Akwanga yayin bikin aza harsashin ginin jami’ar Cibiyar Hulɗar Jama’a ta Nijeriya, inda ya jaddada cewa aikin yana tafiya ne sakamakon ingantattun gyare-gyaren tattalin arziki da na kuɗaɗe da ake aiwatarwa a ƙarƙashin shugabancin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
Ya nuna cewa a baya jihar kan nemi rance domin aiwatar da ƙananan ayyuka, amma a yanzu tana iya ɗaukar manyan ayyuka na Biliyoyin Naira ba tare da jinginar da makomarta ba, lamarin da ya nuna ƙarfafa tsari da ɗa’a a harkar kuɗi.
Gwamna Sule ya ƙara da cewa ya dade yana tara wannan ajiyar kuɗi ne domin amfani da ita ga gwamnati mai zuwa, sai dai mambobin majalisar zartarwa ta jihar suka shawarce shi da a fitar da wani ɓangare domin kafa wannan jami’a ta musamman.
Ya bayyana cewa an riga an biya kashi 50 cikin ɗari na kuɗin kwangilar aikin tun daga wannan ajiyar, tare da tabbatar da cewa sauran kuɗin za a biya su ne daga asusun ajiyar guda ɗaya.
A nasa jawabin, shugaban Cibiyar Hulɗar Jama’a ta Nijeriya, Dakta Ike Neliaku, ya yaba da hangen nesa da kwarewar gwamnan wajen sauya buri zuwa ayyuka na zahiri, yana mai cewa jami’ar za ta sanya jihar Nasarawa a taswirar duniya ta ilimi da horar da kwararru.
Tsohon gwamnan farar hula na farko a jihar, Sanata Abdullahi Adamu, da mataimakin shugaban cibiyar, Farfesa Emmanuel Dandaura, sun bayyana aikin a matsayin tarihi a fannin ilimi, inda suka nuna cewa jami’ar za ta kasance ta farko a Afirka, tare da haɗa gwamnati, masana’antu da jami’o’i a tsari guda.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa aikin haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jihar Nasarawa, Cibiyar Hulɗar Jama’a ta Nijeriya da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.











































