Daruruwan fasinjojin jirgin na Azman ne a safiyar ranar Talata suka mamaye hedikwatar kamfanin domin nuna rashin amincewarsu da soke jirginsu.
Da farko an shirya jirgin Kano zuwa Legas da karfe 7:30 na safe.
Solacebase ta ruwaito cewa fasinjojin da suka yi zanga-zangar da sun koka da rashin jin dadin sokewar da aka yi musu ba zato ba tsammani sun nuna rashin amincewarsu da lamarin saboda babu wata sanarwa kafin daukar matakin.
Fasinjoji biyu, mata da miji da zasu bi jirgin a kan hanyarsu ta zuwa Landan sun nuna takaicin su kan abun da ya faru.
Shima Wani fasinja wanda zai bi jirgin akan hanyar sa ta zuwa Sudan domin neman magani ya bayyana yadda soke jirgin ya haifar masa da matsala, inda ya bayyana cewa zai sanya ya rasa jirgin da zai dauke shi a yau.
Wani dan majalisar dokokin jihar Kano wanda shi ma yana cikin jirgin da aka soke ya ce hakan ya janyo masa cikas kan taro mai muhimmanci da ya yi niyar halarta a Legas.
Babban jami’in tsaro na kamfanin jirgin Bashir Otaru wanda ya yi jawabi ga fasinjojin ya bayyana takaicinsa kan lamarin.
Ya ce an soke tashin jirgin ne saboda wata matsala ta da jirgin ya samu.
Ya ce za a shiryawa fasinjojin wani jirgi a yammacin Laraba, yayin da wadanda ke so a dawo musu da kudinsu za dawo musu da sh.













































