YANZU-YANZU : A karshe APC ta tsayar da ranar gudanar da babban taron ta na kasa

Gov. Buni
Gov. Buni

Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC Mai Mala Buni ya bayyana ranar 26 ga watan Fabrairu a matsayin ranar gudanar da babban taron jam’iyyar APC.

Mai Mala Buni, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Yobe, ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wurin taron matan jam’iyyar APC na kasa na shekarar 2022, wanda aka gudanar a babban dakin taro na kasa ICC da ke Abuja.

Ya ce jam’iyyar tana neman goyon bayan matan jam’iyyar don gudanar da babban taron cikin nasara.

Cikakkun bayanai daga baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here