Rahotanni sun bayyana cewa wata maniyyaciya aikin Hajjin bana yar asalin jihar Zamfara ta haifi jariri a birnin Madina na kasar Saudiyya.
Kungiyar masu aiko da rahotonnin aikin Hajj watau Independent Hajj Reporters of Nigeria ne suka bayyana hakan a ranar Talata ta hanyar wani hoto da suka wallafa a shafinsu na Facebook.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa bisa ka’idojin wadanda hukumomin Najeriya musamman hukumar kula da aikin Hajji NAHCON, mata masu juna biyu ba sa samun damar halartar aikin Hajji, la’akari da lafiyarsu da kuma hana shagaltuwa daga gudanar da ibada saboda renon jariri da kuma shayarwa.
Bugu da ƙari, ciki yana ƙara gamuwa da hatsari da matsalolin lafiya.
SolaceBase ta lura cewa maniyyaciyar da alama ta shammaci hukumomin alhazan Najeriya ko kuma ta kaucewa gwaje-gwajen juna biyu da ake yi ga maniyyata gabanin basu damar tafiya kasa mai tsarki.
Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun hukumar NAHCON kan ci gaban bai yi nasara ba saboda layin wayarta ba ya shiga.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da rahotonni suka ce jami’an Saudiyya sun kama mata da kuma mahaifiyar fitaccen shugaban ‘yan bindigar nan Ado Aliero, da aka cafke su a birnin Madina.













































